Home General Kotun koli ta tabbatar da Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar PDP

Kotun koli ta tabbatar da Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar PDP

Kotun Kolin Najeriya ta soke hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta zartas a baya, na dakatar da na hannun damar Nyesom Wike Sanata Samuel Anyanwu, a matsayin sakataren jam’iyyar PDP na kasa.

A wani hukunci da alkalan kotun mutum biyar suka yanke da mai shari’a Jamilu Tukur ya gabatar, kotun Kolin ya soki kotun ɗaukaka ƙara da babban Kotun jihar Enugu na shiga abin da ta kira rikicin cikin gida.

Tun a baya babbar kotun da ke Enugu ta cire Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar bisa ƙarar da wani ɗan jam’iyyar PDP Mista Aniagu Emmanuel ya shigar.

Hakazalika kotun ɗaukaka ƙara a jihar ta tabbatar da hukuncin babban kotun wanda ya amince da Cif Udeh-Okoye a matsayin wanda ya maye gurbin Sanata Anyanwu a matsayin sakataren Jam’iyya.

Bayan rashin amincewa da hukuncin, Anyanwu ya ɗaukaka ƙarar zuwa kotun ƙoli.

Anyanwu da Sunday Ude-Okoye sun soma rikici kan matsayin sakataren jam’iyyar ne tun bayan da Anyanwu ya bar matsayin domin yin takara a zaɓen gwamnan Imo wanda ya yi rashin nasara.

Bayan rashin nasararsa, ƙoƙarin dawowa kan kujerarsa ya jefa jam’iyyar cikin rikici wanda ya kawo rarrabuwar kai tsakanin ƴan ƙungiyar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp