Home General Kotu ta ɗage shari’ar Nnamdi Kanu bayan cigaba da zama a yau...

Kotu ta ɗage shari’ar Nnamdi Kanu bayan cigaba da zama a yau Juma’a

Jagoran haramtacciyar ƙungiyar ‘yan’aware ta Indigenous People of Biafra (IPOB) ya sake bayyana a gaban babbar kotun tarayya yau Juma’a a Abuja babban birnin Najeriya.

Sai dai ɗaya daga cikin lauyoyinsa Aloy Ejimakor ya ce kotun ƙarƙashin Mai Shari’a James Kolawole ta ɗage cigaba da sauraron ƙarar zuwa 29 ga watan Afrilu da kuma 2 da 6 ga watan Mayu na 2025.

Ci gaba da shari’ar ta Nnamdi Kanu na zuwa ne bayan Alƙaliyar Alƙalai Kudirat Kekere-Ekunnyefere ta saka Mai Shari’a James Kolawole Omotoshi a matsayin sabon alƙalin da zai saurari shari’ar bayan Kanu ya yi ƙorafi kan Mai Shari’a Binta Nyako.

An yi hasashen za a yi bitar tuhuma bakwai da gwamatin Najeriya ke yi wa Kanu yayin ci gaba da shari’ar, waɗanda suka jiɓanci tayar da fitina da kuma ta’addanci.

A watan Disamban 2023 ne Kotun Ƙoli ta umarci Kanu ya koma babbar kotun ta tarayya domin kare tuhumar da ake yi masa bayan Binta Nyako ta yi watsi da takwas cikin 15 da gwamnati ta gabatar a 2021.

Gwamnatin Najeriya ta kai Kanu kotu ne bayan kama shi a wata ƙasar waje a 2021, kuma har yanzu mambobin ƙungiyarsa da gwamnati ta haramta na ci gaba da neman ɓallewa daga Najeiriya domin kafa ƙasar Biafra.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp