Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ayyana makoki kwana uku bayan wasu ‘yanbindiga sun kashe aƙalla mutum 44 yayin da suke sallar Juma’a.
Rahotonni sun ce harin ya jikkata mutum 13, huɗu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali a harin da aka kai garin Kokorou da ke kan iyakar Nijar da Mali da Burkina Faso.
Wata sanarwa da Ministan Harkokin Cikin Gida Mohamed Toumba ya fitar ta ce maharan da ke biyayya ga ƙungiyar Islamic State wato Islamic State in the Greater Sahara (ISGS) ne suka kai harin a ranar Asabar.
“Da misalin ƙarfe 2:00 na rana, daidai lokacin da Musulmai ke yin sallar Juma’a maharan suka kewaye masallacin domin aikata kashe-kashen da ba a saba gani ba,” in ji ministan.
Kazalika, sun cinna wa “kasuwa da gidajen mutane wuta,” kamar yadda ya bayyana.
Kwana biyu kafin wannan hari rundunar sojin Nijar ta ce ta kashe mambobin ISGS 45.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1486 days 11 hours 38 minutes 15 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1468 days 13 hours 19 minutes 40 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com