Home General Ba za mu yi haɗaka da kowa ba – SDP

Ba za mu yi haɗaka da kowa ba – SDP

Jam’iyyar SDP a Najeriya ta yi watsi da yunkurin haɗaka tsakaninta da sauran jam’iyyun adawa da nufin tunkarar zaɓen 2027.

Wannan na zuwa yayin da ake ganin tagomashin jam’iyyar ta SDP ya karu sakamakon sauya shekar da wasu manya ‘yansiyasa a kasar ke yi zuwa cikinta

A makon da ya gabata ne wasu jagororin adawa ƙarƙashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar na babbar jam’iyyar hamayya ta PDP suka sanar da cewa suna wani yunƙuri na ƙulla haɗaka domin kawar da APC a zaɓen 2027.

Sai dai shugaban jam’iyyar na kasa Alhaji Shehu Musa Gabam a hirarsa da BBC ya ce SDP ba za ta haɗe da wata jam’iyya ba.

“Mun faɗa wa duniya cewa mu ba za mu yi maja ba, ba maganan haɗewa domin akwai ƙa’idoji kuma rashin cika ƙa’idojin wata fitina ce,” in ji shi.

Ya ce babu hannun SDP a yunƙurin hadewar jam’iyyun adawa domin a cewarsa jam’iyarsu tana da tsari.

Shugaban SDP ya ce sai dai duk wanda yake son ya shigo ya zo don gina jam’iyyar.

Ya ce tsarinsu shi ne, duk wanda yake son shiga jam’iyyar zai tafi ne mazaɓarsa, daga nan zai iya takarar duk muƙamin da yake so.

Alhaji Shehu Musa Gabam ya bayyana shakku kan haɗakar jam’iyyu a Najeriya inda ya yi zargin yadda jam’iyya mai mulki ke shiga cikin jam’iyyun adawa tana karya su.

“Ba mu san su wane ne da kuma manufofin da za su shigo da su ba, wannan ya sa NWC ya ƙayyade cewa babu maganar maja,” in ji shugaban jam’iyyar SDP.

Ya ƙara da cewa tsarin jam’iyyarsu ya sha bamban da sauran jam’iyyu musamman batun korar ƴan jam’iyya da ake yi daga mazaɓar mutum.

Ya ce shugaban jam’iyya a mazaɓa ba ya da ikon korar mutum sai da amincewar shugabancin jam’iyyar.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai na cikin manyan ƴansiyasar da suka sauya sheƙa zuwa SDP, wanda kuma a wata hira da BBC ya yi wa wasu manyan jagororin adawa tayin sabuwar jam’iyyar tasa.

Shugaban jam’iyyar SDP ya ce akwai ƴansiyasa sama da 200 da suka yi murabus daga jam’iyyunsu suka shigo SDP, sai dai bai bayyana sunayensu ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp