Rundunar ‘Yan sandan Nijeriya ta janye Gayyatar da ta yiwa Sarkin Kano

Sifeto janar na ‘yansandan Najeriya ya janye gayyatar da hukumar ta yiwa Sarkin Kano Sanusi zuwa shelkwatar hukumar domin amsa tamabayoyi.

Umarnin janyewar ya fito ne ta baki mai magana da yawun hukumar Olumuyiwa Adejobi, inda ya ce janyewar ta zama wajibi bayan tsoma bakin da masu ruwa da tsaki suka yi a kasar, yana mai cewa hakan yayi daidai da tsarin aikinsu na tabbatar da aiyukansu ba a siyasantar dasu ko fahimtarsu a baibai ba.

Saidai sanarwar ta umarci kwamishinan ‘yansandan jihar da ya karbi bayanan binciken sarkin a jiharsa ta Kano.

Tun da fari dai rundunar ‘yan sandan ta kasa ta gayyaci Khalifa Muhammadu Sanusi ne bisa zargin karya dokar da ta saka na haramta yin dukkan wani hawa a cikin bukukuwan sallah Karama.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com