Home General An sake kama wasu mafarauta ƴan Kano a Jihar Edo

An sake kama wasu mafarauta ƴan Kano a Jihar Edo

Jami’an ƙungiyar tsaron Jihar Edo sun sake kama wasu mafarauta hudu daga Kano, a yayin da suka damƙasu rundunar ‘Yansandan jihar, kama mafararutan ya zo ne makonni kadan bayan kisan gilla da ’yan bangar Jihar Edo suka yi wa ayarin wasu mafarauta 16 daga jihar Kano a jihar.

Rundunar ’Yansandan Jihar Edo, ta ce mafarautan da aka kama sun fito ne daga Karamar Hukumar Doguwa ta Jihar Kano, kuma suna dauke da bindigogin toka ne guda uku, da adduna da wukake a lokacin da aka kama su.

Kakakin ’yan sanda an jihar, CSP Moses Yamu, ya ce kanawan da aka kama mafarauta ne ba kamar yadda ake yadawa a kafofin sada zumunta cewa makiyaya ba ne.

Ya bayyana cewa jami’an kungiyar tsaro ta Jhar Edo ne suka kama mafarautan sannan suka damka su ga ’yan sanda inda ake yi musu tambayoyi a ofishin ’yan sanda da ke yankin Ikpoba Hill.

Ya ce “An kama mafarautan da suka fito daga Karamar Hukumar Doguwa ta Jihar Kano a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa yankin Uvbe da ke Karamar Hukumar Orhionwon a Jihar Edo. A halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike.”

Da haka Kwamishinan ’yan sandan jihar, Monday Agbonika, ya gargadi jama’ar jihar da su guji yada abin da ba gaskiya ba ne game da lamarin, domin yana iya tayar da zaune tsaye.

Idan ba a manta ba, a cikin watan Ramadan, gab da Karamar Sallah ne ’yan banga suka yi wa wasu mafarauta 16 daga Jihar Kano da ke hanyarsu ta komawa gida hutun sallah kisan gilla a yankin Uromi da ke jihar, lamarin da ya haifar da tayar da jijiyoyin wuya, inda har yanzu ake kokarin shawo kansa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp