Zanga-zangar Ma’aikatan hukumar Nimet a filin jirgin saman Malam Aminu Kano dake jihar kano a Arewa maso yammacin Nijeriya ya dakatar da sauka da tashin jiragen sama filin.
Ma’aikatan hukumar sun gudanar da zanga zangar ne bisa abin da suka kira da jan kafa wajen fara biyan su mafi karancin albashi kamar yadda gwamantin tarayyar Nijeriya ta amince da shi.
Read Also:
A wata ganawa da da jaridar Global tracker ta yi da shugaban kungiyar gamayyar kungiyoyin ma’aikatan na shiyyar arewa maso yammacin Nijeriya Timoty Meshelia, yace baya ga rashin biyan su mafi karancin albashin, akwai kuma hakkokin ma’aikatan na alawus alawus da aka gaza biya.
Kungiyar ta bawa hukumar gudanar filin jirgin saman na Malam Aminu Kano wa’adin wata guda da ta dauki matakan da suka dace wajen magance matsalolin tattalin arziki da ma’aikatan ke fuskanta da suka hadar da biyan su alawus-alawus da kuma samar musu da ingantaccen yanayin aiki.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1485 days 19 hours 3 minutes 54 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1467 days 20 hours 45 minutes 19 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com