Home General Ghana ta kora ƴan Najeriya sama da 200 zuwa gida

Ghana ta kora ƴan Najeriya sama da 200 zuwa gida

Gwamnatin Najeriya ta karbi ƴan asalin ƙasar guda 231 da ƙasar Ghana ta koro, 204 daga cikin su fasa ƙwaurinsu akayi zuwa ƙasar.

Bayanai sun ce mutanen sun sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na jihar Lagos, ƙarƙashin tarbar hukumar yaƙi da fasa kwaurin ɗan adam ta ƙasar, da kuma hukumar kula da ƴan Najeriya da ke ƙetare da haɗin gwiwar hukumar yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ta’annati da shirya laifuffuka ta Ghana.

Da yake Magana yayin karɓar mutanen, shugaban hukumar yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ta‘annati da shirya laifuffuka na Ghana Dominic Mensah yace an kama mutanen ne bayan da jami’an tsaro suka bankaɗo wani tuggun shirin aikata laifi a wani rukunin gidaje guda 50 a ƙasar ta Ghana.

Yace tuni jami’an tsaro suka kama mamallakin gidajen don ci gaba da bincike, yayinda ƴan Najeriyar kuma aka yanke shawarar mayar da su gida.

Cikin mutane 204 da aka dawo da su guda 76 yan asalin jihar Edo ne, sai guda sauran da suka fito daga jihohin Anambra, Delta, Bayelsa, Imo, Enugu, Ebonyi da sauran wasu jihohi.

Wani abu mai tada hankali shine yadda 12 daga cikin mutanen ke zaman ƙananan yara ƴan kasa da shekara 18.

Da take mayar da martani kan wannan batu, shugabar hukumar kula da ƴan Najeriya mazauna ƙetare, Abike Dabiri Erewa ta ce ƴan Najeriya na bukatar wayar da kai na musamman game da illar fasa ƙwaurin ɗan adam da kuma shiga wata ƙasa ba bisa ƙa’ida ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp