Aƙalla mutane 28 cikin su har da masu hakar ma’adinai 20 ne ƴan bindiga suka kashe a ranar Alhamis da ta gabata a yayin wasu jerin hare-hare da suka kai ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya.
Hare-haren sun auku ne da misalin ƙarfe 11 da rabi na safe akan garuruwan Gobirawa Chali, Damaga da Lugga, hare-haren da mazauna yankunan suka ce sun zo musu a bazata, inda ɗimbin yan bindiga suka kutsa garuruwan nasu a lokaci guda.
Kamfani dillancin labarai na Reuters ya ruwaito wani mazauna garin yana cewa ƴan bindigan sun bude wuta akan masu haƙar ma’adinai, kuma nan ne rikici ya ɓarke har mutane da dama suka mutu.
Read Also:
A wata sanawar da ta fitar a wannan Juma’a, ƙungiyar kare hakkin ɗan adam ta Amnesty ta tabbatar da harin, tana mai cewa maharan sun bi gida-gida a garin Gobirawa Chali, inda suka kashe sama da mutane 20.
A garin Damaga kuwa, mutane biyar ne maharan suka kashe, ayayin da uku suka gamu da ajalinsu a garin Lugga.
Wani mazaunin Lugga ya bayyana yadda ƴan bindigar suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi a kewayen ƙauyen, kana suka yi awon gaba da dabbobi.
Rahotanni sun ce dakarun rundunar sojin ƙasar sun kawo ɗauki ba tare da ɓata lokaci ba, abin ma da ya taƙaita ɓarnar kenan.
Dakarun ƙasa da jiragen yaƙin sun shiga garin a yayin harin, inda suka yi bata – kashi, wanda ya kai ga mutuwar ɗimbin maharan.
Waɗannan hare-hare su na nuni da yadda ake cigaba da samun matsalar tsaro a jihar Zamfara, inda ƴan bindiga suka addabi ƙauyuka da dama, duk kuwa da aikin da sojoji ke yi a yankin.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1462 days 9 hours 18 minutes 52 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1444 days 11 hours 17 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com