Home General An naɗa sabon kwamandan da zai jagoranci yaƙi da Boko Haram a...

An naɗa sabon kwamandan da zai jagoranci yaƙi da Boko Haram a Najeriya

Rundunar sojojin Najeriya ta naɗa Manjo Janar Abdulsalam Abubakar a matsayin sabon kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, wacce ke yaƙi da masu tada kayar baya a yankin arewa maso gabas ƙasar, bayan yawaitar kai hare-hare cikin watanni huɗu da suka gabata, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da sojoji da dama a yankin.

A cikin wata sanarwa da kakarin rundunar Reuben Kovangiya ya fitar, ta ce Janar Abubakar ne kwamandan rundunar na 15 da ke yaƙi da mayaƙa Boko Haram da kuma ISWAP a shiyar Arewa maso gabashin ƙasar.

A ƴan makonnin nan dai , mayaƙan Boko Haram da kuma ISWAP sun zafafa kai hare-hare a shiyar, lamarin da ya haifar da fargaba wajen sake dawowar mayaƙar masu iƙirarin jihadi, waɗanda ke amfani da ababen fashewa akan hanyoyi da dai-dai sauransu wajen kai hari.

Ko a jiya Talata sai da ƙungiyar ISWAP ta yi iƙirarin ɗaukar nauyin harin da aka kai jihar Borno da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 26, ciki harda mata da ƙananan yara.

Sai dai sanarwar bata alaƙanta naɗin Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, da sabbin hare-haren da masu tada ƙayar bayan ke kaiwa a ƴan kwanakin nan ba.

Sama da shekara 15 ke nan sojojin Najeriya suka kwashe wajen yaƙi da masu tada ƙayar baya a shiyar Arewa maso gabashin ƙasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp