Home General Gwamnoni za su fitar da dabarun yaƙi da matsalar tsaro a Arewa...

Gwamnoni za su fitar da dabarun yaƙi da matsalar tsaro a Arewa Maso Gabashin Najeriya

Ƙungiyar gwamnonin Arewa Maso Gabashin Najeriya ta ce za ta yi amfani dabaru daban-daban ta ƙarfi da lalama wajen tunkarar matsalolin tsaro da suka addabi yankin.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne cikin bayanin bayan taro da gwamnan Taraba Agbu Kefas ya karanta bayan kammala taronsu karo na 11 a Damuturun jihar Yobe.

Gwamnonin sun ce dole ne a kawo ƙarshen matsalar rashin ayyukan yi na matasa, rashin ilimi mai inganci, rashin ababen more rayuwa da kuma sauran matsalolin da ke da alaƙa da talauci idan har ana son kawar da matsalar tsaro.

Yayin da zauren ke jinjinawa gwamnatin tarayyar ƙasar kan ƙoƙarinta a yaƙi da matsalar, ya kuma nuna damuwa game dawowar ayyukan ‘yan bindiga a wasu sassan yankin, a don haka su ka yi kira da jami’an tsaro da shugabannin al’umma su sake nazari kan dabarun yaƙi da matsalar.

Gwamnonin sun kuma nuna damuwa kan lalacewar manyan titunan ƙasar, wanda hakan ke ƙara ta’azzara matsalar tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziƙi.

Ƙungiyar ta kuma ƙudiri aniyar ƙarfafa dangantakar mambobinta domin bunƙasa harkokin noma, makamashi, bayar da horo domin rage rashin aikin yi na matasa, da kuma tunkarar matsalolin sauyin yanayi.

Taron wanda gwamnan Borno kuma shugabansa Babagana Zulum ya jagoranta, ya samu halartar gwamnonin Adamawa, Borno, Gombe, Taraba da Yobe, yayin da na Bauchi mataimakinsa ya wakilce shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp