Mayaƙan Boko Haram sun hana gudanar da Sallar Juma’ar a Kamaru

Rahotanni daga ƙasar Kamaru sun ce barazanar kai harin mayakan Boko Haram a garin Garwa ya sanya hana Sallar Juma’ar da aka saba gudanarwa a yau, abin da ya jefa jama’a cikin ruɗani.

Bayanan sun ce tun da safe aka yi ta yaɗa labarin shirin kai harin ƴanta’addan, waɗanda suka zafafa hare-harensu a ƴan kwanakin nan, wannan ta sa shugabanni ɗaukar matakin dakatar da Sallar Juma’ar domin kare lafiyar jama’a.

Cikin manyan Masallatan da aka rufe yau har da Masallachin tsohon shugaban ƙasa Ahmadu Ahidjo.

Wakilin RFI hausa a Garwa Rilwanou Shehu Ousmane ya tabbatar da aukuwar lamarin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com