Birtaniya ta yaba wa Tinubu kan tsare-tsaren tattalin arziƙi

Gwamnatin Birtaniya ta ce matakan da shugaban Najeriya bola Ahmed Tinubu ke ɗauka a ɓangaren tattalin arzikin ƙasar kwalliya na biyan kuɗin sabulu.

Birtaniyan ta ce matakan da aka ɗauka musamman wajen farfaɗo da darajar kuɗin ƙasar, da na kuɗin shiga na daga cikin dalilan da suka aka samu ƙaruwar damar zuba jari a ƙasar.

Jakadan Birtaniya a Najeriya Dr. Richard Montgomery ne ya sanar da hakan a yayin wani taro na aiwatar da shirin bunƙasa tattalin arzikin Najeriya da Birtaniya, ta fuskar kasuwanci da zuba jari tsakanin ƙasashen biyu, da ya gudana a Abuja babban birnin na Najeriya.

Gwamnatin Birtaniyar ta ce la’akari da rahoton da Bankin Duniya a baya-bayan nan kan harkokin zuba jari a Najeriya ya nuna cewar darajar kuɗin ƙasar naira na farfaɗowa.

Haka kuma rahoton ya ce ana samun ƙaruwar kuɗaɗe a asusun ƙasashen wajen na ƙasar da kuma na haraji, lamarin da ya sa ake samun buƙatar ƙara faɗaɗa harkokin zuba jari a ƙasar.

Birtaniyan ta ce shirin bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen biyu da suke haɗin gwiwa za a cimma shi ne idan Najeriya ta mayar da hankali kan wajen samar da daidaitacen tsari da zai haɓaka harkokin kasuwanci da janyo hankulan masu zuba jari a ƙasar.

Sai dai ya ce ganin irin matakan da shugaban Najeriya ya ɗauka a ɓangaren tattalin arzikin ƙasar, yasa suka fitar da wasu ɓanagarori takwas da zasu haɗa gwiwa da Najeriya wajen ganin ta haɓaka kasuwacin da yawan masu zuba jari a ƙasar.

Haka kuma Jakadan Birtaniyar ya ce baiwa kamfanonin ƙasar irin na su Ɗangote suka fara tace man fetur yasa an samu raguwar fitar da ɗanyen man fetur zuwa ƙasashen waje.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1462 days 4 hours 1 minute 14 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1444 days 5 hours 42 minutes 39 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com