Home General JAMB ta saka ranar sake jarrabawa a wasu cibiyoyin

JAMB ta saka ranar sake jarrabawa a wasu cibiyoyin

Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta Najeriya, Jamb ta amince da saka sabuwar ranar sake jarrabawar UTME ga wasu ɗaliban da suka yi jarrabawar a wasu cibiyoyin rubuta jarrabawar.

A wani taron manema labarai da shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede, ya gabatar a Abuja, babban binrin ƙasar ya ce hukumar ta amince da matsalolin da aka samu a jarrabawar UTME ta 2025,

Ya ƙara da cewa ɗalibai 206.610 ne za su sake jarrabawar a cibiyoyi 65 a Legas, yayin da a Owerri ɗalibai 173,387 za su sake jarrabawar a cibiyoyi 92.

Za a fara sake jarrabawar daga ranar 16 ga watan Mayu, inda za a aike da saƙon waya ga ɗaliban da lamarin ya shafa.

Shugaban hukumar ya kuma nemi afuwar ɗaliban kan matsaloli da aka fuskanta a lokacin jarrabawar.

“Na ɗauki alhakin duk abin da ya faru, kuma ina bayar da haƙuri ga ɗaliban da lamarin ya shafa”, in ji Farfesa Oyodele.

Farfesa Oloyode ya ce matsalar na’ura da aka samu a wasu santocin jihohin Legas da Owerri sun haifar da ƙorafe-ƙorafe daga wasu ɗaliban, inda hukumar ta gano matsalar bayar fitowar sakamakon jarrabawar.

“Matsalar ta samo asali ne daga ɗaya daga cikin kamfanonin da ke bai wa hukumarsu sadarwar, wanda jami’ansa suka kasa magance matsalar ta yadda hakan ya shafi wasu cibiyoyin rubuta jarrabawar,” in ji shugaban hukumar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp