Jam’iyyar PDP ta bukaci Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya koma cikinta.
Shugabar Matan Jam’iyyar ta shirya Arewa maso yammaci Amb. Zainab Audu Bako ce ta yi kiran yayi da take ganawa da manema labarai a jihar Kano.
Amb. Audu Bako ta ce Gwamnan Kano na da managarta halaye tun yana rike da mukamin Kwamishina,
Read Also:
“Matsayina na tsohuwar Kwamishina nasan irin Jajircewarsa yanzu kuma gashi yana Gwamna yakan baza kunnuwansa kasa domin jin koken Al’umma.
“Haka shugaba na gari ya kamata ya zama.
“Don haka kayi watsi da korayen korayen da ake maka na koma Jam’iyyar APC tun da ita kuma Jam’iyya NNPP rikici ya yi mata yawa.