Shugaba Bola Tinubu ya ce Najeriya ta kama hanyar inganta kuma lokacin matsi ya wuce.
A jawabinsa na cika shekara biyu da karɓar ragamar mulki, Tinubu ya amince cewa tsare-tsarensa na kawo gyara sun janyo matsi kuma bai raina haƙuri da kuma uzurin da ƴan Najeriya suka nuna masa ba.
“A yau ina alfahari cewa sauye-sauyen mu a fannin tattalin arziki suna aiki. Mun kama hanyar samar da ƙasa mai ƙarfin tatalin arziki,” in ji shi.
A ranar da aka rantsar da shi a cikin watan Mayun 2023, shugaba Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur da aka daɗe ana cece ku-ce a kai, lamarin da ya janyo tsadar rayuwa a ƙasar.
Tinubu ya ce: “Duk da tsadar rayuwa da muka faɗa, mun samu ci gaba sosai. Hauhawar farashi ta fara raguwa musamman a kan farashin shinkafa da sauran kayayyaki.”
Alƙaluman da hukumomi suka fitar sun nuna cewa hauhawar farashi ya ƙaru zuwa kashi 24 cikin ɗari a watan da ya gabata, idan aka alaƙanta da kashi 22 da ake ciki a lokacin da Tinubu ya karɓi mulki.
A haka ma an samu raguwa ne idan aka kwatanta da kashi 34 da aka samu a shekarar da ta gabata, lamarin da ya janyo zanga-zanga a sassan ƙasar har ta kai ga asarar rayuka.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1485 days 23 hours 10 minutes 5 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1468 days 51 minutes 30 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com