Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da fara biyan kudaden tsofaffin kansilolin da suka yi lokacin tsohuwar gwamnatin APC da Kudi sama da Naira Biliyan 16.
Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da al’amuran cikin gida na jihar kano Com. Ibrahim Abdullahi waiya ya fita aka raba manema labarai a jihar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya cika alƙawarin da ya ɗaukarwa tsofaffin kansilolin da sukai mulki a lokacin gwamnatin Ganduje, na fara biyan haƙƙokin su wanda yace Abdullahi Ganduje ya nuna halin ko in kula dasu lokacin da yake kan mulki.
Waiya ya ƙara da cewa rukunin kansilolin da suka fito daga ƙananan hukumomi 44 daga kuma mazaɓu 484 gaba ɗayan su zasu karɓi haƙƙokin nan ba jimawa ba.
A karan farko dai kansiloli 903 ne suka amfana da naira biliyan ɗaya da miliyan ɗari takwas ₦ 1.8. waɗanda sukai aiki daga shekarar daga 2014 zuwa 2017.











