Rundunar ƴansanda a jihar Kano ta ce ta kama mutane 41 da ake zargi da hannu a kisan baturen ƴansanda na Rano, CSP Baba Ali.
Kwamishinan ƴansanda a jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce kisan jami’in nasu babban abin takaici da tashin hankali ne.
Kisan jami’in ya janyo suka daga ɓangarori da dama, musamman a lokacin da bidiyon mummunan al’amarin ya riƙa yawo a shafukan sada zumunta.
A cikin sanarwar da rundunar, reshen jihar Kano ta fitar a yau Alhamis, kwamishinan ƴansandan ya ce rundunar tana yin duk abin da ya dace domin ganin an gurfanar da masu hannu a kisan jami’in nata da kuma tabbatar da cewa sun fuskanci hukunci daidai da abin da suka aikata.
Rundunar ta kuma buƙaci jama’a su ci gaba da gudanar da harkokin su na yau da kullum, yayin da jami’an rundunar ke ci gaba da aikin zaƙulo masu hannu a kisan da ma sauran laifuka domin su fuskanci hukunci.