Dakarun sojin Najeriya na Operation Haɗin-Kai sun ce sun kashe ƴan ta da ƙayar-baya sama da 60 a wani artabu da suka yi a jihar Borno.
Wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta fitar ranar Juma’a, ta ce dakarun sun samu nasarar kashe ƴan ta’ddan ne bayan bata-kashi da suka yi daddare a yankin Bita na jihar.
Sanarwar ta ce ƴan ta da ƙayar-bayan sun far wa sojojin birget 26 ne da misalin karfe 1:09 na asubahin yau Juma’a, inda dakarun Haɗin-Kai suka mayar da martani da hare-hare ta sama da kuma ƙasa kan ɓata-garin.
“Sojoji sun kaddamar da hare-haren sama da kuma ta ƙasa kan sansanonin ƴan ta da ƙayar baya a yankin Bita na jihar Borno da asubahin yau Juma’a, lamarin ya kai ga hallaka aƙalla 60 daga cikinsu,” a cewar sanarwar sojojin.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1485 days 14 hours 40 minutes 43 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1467 days 16 hours 22 minutes 8 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com