Sojojin Najeriya sun kashe manyan kwamandojin Boko Haram da ISWAP

Nigerian Army

Rundunar sojojin Najeriya ta samu gagarumar nasarar kashe manyan manyan kwamandojin Boko Haram da na tsagin ISWAP, a wasu hare-hare da ta kai a makon da ya gabata da kuma wannan makon da mu ke ciki.

A wasu hare-hare da sojojin da ke aiki a ƙarƙashin rundunar Operation Hadin Kai suka kai garuruwan Mallam Fatori da kuma Buratai na jihar Borno a makon da ya gabata, sun samu nasarar kashe kwamandojin Boko Haram uku da suka haɗa da Amir Abu Ali da Amir Ibunu sai kuma Amir Abu Waldume.

Haka nan a wani harin na daban da suka kai Nzalgana na jihar Yobe da kuma Timbuktu na jihar Borno, jami’an tsaron na Najeriya sun kashe Ameer Malam Jidda, ɗaya daga cikin manyan kwamandojin Boko Haram a garin Ngorgore da Malumti.

Kisan manyan jagororin Boko Haram da sojojin Najeriya suka dai ya raunata tsarin shugabancinsu da kuma sanyasu cikin ɗimuwa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com