Home General Wani kamfani zai fara samar da kayan gwajin cutar HIV da kuma...

Wani kamfani zai fara samar da kayan gwajin cutar HIV da kuma Malaria a Najeriya

Wani kamfanin samar da magunguna a Najeriya Codix Bio, na shirin samar da kayayykin gwajin cuta mai karya garkuwar jiki da kuma Malaria, biyo bayan matakin Amurka na janye bada tallafin irin waɗannan kayayaki da ake bayarwa.

Amurka ce ƙasar da ta fi kowacce bai wa hukumomin lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya talafi, saboda haka ƙasashe masu tasowa ke kan hanyar tagayyara matukar ba a sami wata hanyar samar da kayayyskin lafiyar ba.

Wannan lamari dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ƙasar ke ƙoƙari, wajen kawo ƙarshen cutar zazzaɓin cizon sauro da kuma rage yawan masu kamuwa da cuta mai karya garkuwar jiki.

Bayanai sun ce kamfanin na da ƙarfin da zai iya samar da kayayykin gwajin guda miliyan 147 duk shekara, amma sannun a hankali zai iya kaiwa miliyan 160.

A cewar shugaban kamfanin Olanrewaju Balaja, matukar aikin ya sami nasarar da ake bukata, kamfanin zai faɗaɗa ayyukan sa zuwa sauran sassan Africa, musamman ƙasashen kudu da hamada.

Kawo yanzu dai babu bayani ƙarara kan yadda Najeriya za ta ji jiki da matakin na Amurka, amma mahukunta sun ce sun kara yawan kuɗaɗen da suke warewa ɓangaren lafiya don cike gibin janye tallafin da Amurka ta yi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
COAS Ya Bukaci Bojojin Nijeriya da su Mayar da Hankali Wajen Kare Rayukan Fararen HulaTURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci MatsalolintaDangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige Fubara
X whatsapp