Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da zargin yin biris da ƴan ƙasarta dake Iran dai-dai lokacin da yaƙi ke ƙara rinchaɓewa a tsakanin Isra’ila da Iran ɗin.
A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Kimiebi Imomotimi Ebienfa ta ce zargin bashi da tsuhe ballantana makama.
Read Also:
A cewar sanarwar gwamnatin Najeriya, ƙarƙashin ma’aikatar harkokin waje na iya bakin ƙoƙarinta don tabbatar da cewa ƴan Najeriya mazauna Tehran na cikin ƙoshin lafiya.
Sanarwar ta ci gaba da cewa an baiwa ma’aikatan da ke yiwa gwamnatin Najeriya aiki a Iran damar aiki daga gida, sakamakon hare-haren da ke faɗawa sassan birnin.
Ma’aikatar harkokin wajen ta kuma ƙara da cewa tuni gwamnati ta fara aiki tare da gwamnatin Armenia don duba yadda ƴan Najeriya mazauna Iran ɗin zasu tsallaka ƙasar don samun mafaka.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1486 days 16 hours 35 minutes 58 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1468 days 18 hours 17 minutes 23 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com