Tinubu ya jajanta wa al’ummomin Kaduna da Kano da kuma Borno kan mutuwar mutanensu

Shugaba Bola Tinubu ya yi Alla-wadai da kisan wasu matafiya 12 a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato a hanyarsu ta zuwa ɗaurin auren ɗan’uwansu.

Ya buƙaci jami’an tsaro su tabbatar da kama masu laifin tare ganin an hukunta su.

Wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara kan harkokin yaɗa labaru Bayo Onanuga ya fitar ranar Lahadi, shugaban ya ce ba za su lamunci aikata irin haka ba.

“Kowane ɗan ƙasa na da ƴancin yin tafiya zuwa kowane ɓangare na ƙasar nan,” in ji Tinubu.

Ya jajanta wa iyalan waɗanda aka kashe da kuma gwamnatin jihar Kaduna, inda ya yi kira da a kwantar da hankali tare da alkawarin cewa sai an hukunta maharan.

A ɗaya gefen, Tinubu ya nuna kaɗuwa kan mutuwar wasu mutum 10 da ƴar ƙunar bakin wake ta hallaka a babbar kasuwar kifi da ke karamar hukumar Konduga na jihar Borno ranar Asabar.

Ya miƙa sakon ta’aziyyarsa ga gwamnati da kuma al’ummar jihar kan lamarin da ya faru.

“Na bai wa jami’an tsaro umarnin matsa ƙaimi don farauto ƴan Boko Haram da suka rage don daƙile ayyukansu. Na kuma bai wa hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA umarnin tallafawa waɗanda abin ya shafa,” in ji shugaban Najeriyar.

Har ila yau, ya sake miƙa ta’azziyarsa ga mutum biyar da suka mutu a wata fashewa a jihar Kano.

Ya buƙaci hukumomi su gudanar da bincike don gano abin da ya haddasa fashewar tare da ɗaukar matakan da suka dace don kare afkuwarsa a gaba.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1486 days 10 hours 13 minutes 39 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1468 days 11 hours 55 minutes 4 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com