Home General Waɗanda suka tsira daga kisan Filato sun bayyana yadda sojoji suka cece...

Waɗanda suka tsira daga kisan Filato sun bayyana yadda sojoji suka cece su

Wasu daga cikin waɗanda suka tsira daga kisan da aka yi wa wasu da za su je biki a Filato sun bayyana wa jaridar Daily Trust yadda aka kai musu hari a lokacin da suke tafiya zuwa bikin aure.

Ibrahim Umar, ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira, ya ce suna kan hanyarsu ne daga Zariya zuwa Qua’an Pan domin bikin ɗan uwansa. A cikin motar akwai mahaifin ango, kawunsa da kuma ƙaninsa. Duk da cewa sun bayyana wa maharan cewa ba ‘yan yankin ba ne, kuma suna ɗauke da goro da kyaututtukan biki, sai ya ce, “ba su saurare mu ba – suka kashe ƴanuwanmu.”

Ya bayyana cewa mahaifi da ƙanin ango da kuma kawunsa duk an kashe su a harin.

Angon, wanda asalinsa daga Zariya ne kuma malami ne a wata makaranta a yankin, ya hadu da matar da zai aura a lokacin da yake koyarwa, sannan suka amince su yi aure. Ibrahim ya ce sun bayyana wa maharan cewa ba mazauna yankin ba ne, daga Jihar Kaduna suka taho domin halartar biki, amma ba su yarda ba “Dukkanmu dangin juna ne, daga ƙauye ɗaya muka fito,” in ji shi.

Ibrahim ya ce da ba don sojojin da ke kusa da inda lamarin ya faru sun hanzarta zuwa ba, da abin zai fi muni. “Sojojin sun iso da wuri kuma suka cece mu. In ba don hakan ba, da labarin zai canza,” in ji shi.

Wani, wanda shi ma ya tsira daga harin, Sa’adu Abdullahi, ya bayyana cewa sun yi ɓatan hanya ne suka shiga wani ƙauye ba da gangan ba. Bayan sun tsaya domin tambayar hanya, sai kwatsam aka fara kai musu hari.

Duk da cewa sun shaida wa mutanen cewa suna kan hanyar zuwa biki ne, hakan bai sa aka kyale su ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp