NNPCL ya ƙara farashin litar man fetur

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya ƙara farashin litar mai daga naira 910 zuwa naira 945 a gidajen mansa da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

Haka kuma kamfanin ya ƙara farashin litar mai a gidajen mansa da ke Legas daga naira 870 zuwa 915, kamar yadda rahotanni suka nuna.

Wannan ƙarin ya nuna an ƙara naira 35 a kowace lita a Abuja, da kuma ƙarin naira 45 a Legas.

Jaridar Daily Trust mai zaman kanta ta ruwaito cewa tuni wasu gidajen man suka fara sayar da fetur ɗin a sabon farahi, inda ta ruwaito gidan man NNPCL da ke babbar hanyar Fin Niger Badagry ya fara sayar da man a naira 915.

Haka kuma a gidan man kamfanin NNPCL da ke yankin Kubwa na Abuja, tuni aka fara sayar da man a naira 945.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com