Home General Ba mu warware rawanin Wazirin Adamawa Atiku Abubakar ba – Umar Fintiri

Ba mu warware rawanin Wazirin Adamawa Atiku Abubakar ba – Umar Fintiri

Sakamakon mahawara mai zafi da kuma sukar da ta biyo bayan sabuwar dokar masarautun jihar Adamawa dake Najeriya, wadda aka ce ta tube rawanin Wazirin Adamawa Atiku Abubakar, gwamnan jihar Umaru Fintiri ya ce ba haka lamarin yake ba.

Fintiri wanda ya yi watsi da zargin cewar an yi dokar ce domin musgunawa wasu masu rike da sarautar gargajiya a jihar, cikin su harda tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ya ce babu wani mai sarauta da aka sauke yanzu haka.

Gwamnan ya ce Lamidon Adamawa ne zai fayyace matsayin sarautar Atiku na Wazirin Adamawa da kuma makomarsa kamar yadda sabuwar dokar masarautun jihar ta tanada.

Fintiri ya ce Wazirin Adamawa sarauta ce kawai, amma baya daga cikin masu zaben Sarki ko kuma zama mukami na biyu bayan Lamidon Adamawa.

Gwamnan ya ce Masarautun jihar ce za su tantance masu zaben sarki da kuma ƴan majalisar sa daidai da sabuwar dokar da aka yi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp