Ranar 1 ga watan Janairun 2026 ne za a fara amfani sabbin dokokin haraji a Najeriya

Shugaban hukumar tara kuɗaɗen haraji ta Najeriya Zacch Adedeji, ya ce a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2026 ne sabbin dokokin tattara harajin da shugaban ƙasar ya sanyawa hannu a jiya ne za su fara aiki.

Ya ce tazarar watanni shidan da aka samu, zai baiwa gwamnati damar shiryawa da wayar da kan al’umma da kuma daidaita kasafin kuɗin ƙasar.

Bisa la’akari da yadda ake gudanar da al’amura, idan aka samu irin wannan sauyi, yana ɗaukar lokaci kafin duk masu ruwa da tsaki a ɓangaren su sauya tsarin da ake amfani da shi.

Adedeji ya jaddada mahimmancin fara amfani da sauye-sauyen a farkon shekara, yana mai cewar hakan zai baiwa masu ruwa da tsaki damar aiwatar da shi yadda ya kamata saɓanin a tsakiyar shekara.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com