Rahotonni daga jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya na cewa ƴanbindiga sun kai harin kwanto ɓauna kan wasu ƴan banga tare da kashe aƙalla 70 a wasu ƙauyukan jihar biyu.
Wani mazaunin garin Kukawa da ke jihar na cewa fiye da ƴan banga 60 aka kashe a garin.
Can ma a ƙauyen Banyun na jihar wani mazaunin yankin ya tabbatar wa jaridar kashe ƴan banga 10.
Ya ƙara da cewa maharan sun kuma ƙona gidaje da dama da dukiyoyi.
Bayanai na cewa tun bayan da hare-hare suka yawaita a wasu yankunan Wase, aka riƙa gayyato ƴan banga daga wasu yankunan jihar da ma jihar Taraba domin taimaka wa tsaron wasu ƙauyukan yankin.