Wani harin sojin saman Nijeriya ya yi sanadiyyar mutuwar ayarin ‘Yantadda a hanyar Kebbi zuwa Zamfara
Rundunar Sojin saman Nijeriya karkashin dakarun Operation FANSAN YAMMA sun sami nasarar tarwatsa ayarin ‘yanta’adda dake kan hanyar Kebbi zuwa Zamfara a Arewa maso yammacin Nijeriya.
Wannan na cikin wata sanarwa da daraktan yada labara da hulda da jama’a na rundunar sojin saman Nijeriya Air Commodore Edward Gabkwet ya aikewa PRNigeria a ranar laraba.
Ya ce bayan samun bayanan sirri da rundunar ta yi na cewa ‘yan ta’addan na kokarin yin wani ayari na akalla Babura 150 ko wane dauke da bindigu guda 2 a kusa da kauyen Yarbuga dake karamar hukumar Maru a jihar zamfara domin gudanar da ayyukan ta’addanci a yankin.
Read Also:
Bayan tabbatar da rahoton dakarun rundunar suka gudanar da hari kan ayarin ‘yan bindiga, wanda ya yi sanadiyar hallaka da dama tare da raunata wasu, wadanda suka gudu cikin daji da raunika harbi a jukkunansu, tare da barin tarin makama da baburan hawa, rahotannin daga rundunar na bayyana cewa yanzu haka dakarun rundunar sun tare dukkannin hanyoyi domin hana musu guduwa.
Haka kuma rana 10 ga watan Yuni dakarun sun fantsama cikin kauyen na Yarbuga inda suka sake yin wata arangama, wanna ya basu nasarar gano sauran ‘yanta’addan da suka gudu da runuka a jikin su tare da kone baburansu da kuma kwato makamai.
Gabkwet ya bayyana cewa wannan hari na daga cikin kokarin da dakarun suke na tabbatar da kawo karshen tashin hankalin dake faruwa a yankin Arewa Maso yammacin Nijeriya tare da tabbatar da tsaron rayukan Al’ummar.
Daga PRNigeria
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1490 days 8 hours 20 minutes 14 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1472 days 10 hours 1 minute 39 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com