‘Yan bindiga sun kai wani sabon hari a ƙaramar hukumar Riyom ta jihar Filato, tare da kashe aƙalla manoma 27, a wani yanayi da hare-hare ke ci gaba da zafafa a jihar ta Arewacin Najeriya.
sun bayyana cewa tuni aka garzaya da mutanen da suka tsira da raunuka zuwa asibitin koyarwa na garin Jos da kuma sauran wasu asibitocin a cikin jihar.
Read Also:
Dalyop Solomon, shugaban ƙungiyar matasan Birom ta BYM ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, a cewarsa maharan sun kutsa yankin ne wurin ƙarfe 5:30 na Asuba a ranar Litinin, inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi tare da cinnawa gidaje wuta.
Shugaban ya tabbatar da mutuwar mutane 27, inda ya ce za’a sanar da lokacin jana’izarsu nan gaba, yayin da da dama suka jikkata kuma aka garzaya dasu asibiti.
Tuni ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta barranta kanta daga harin.
Shugaban ƙungiyar na Filato, Ibrahim Babayo ya ce ko kusa basu da hannu a kai harin, yana mai cewa zarginsu da ake bashi da tushe ballantana makama.
Har zuwa wannan lokaci dai gwamnati ba ta ce komai kan harin ba, a wani yanayi da jihar ta tsakiyar arewacin Najeriya ke ci gaba da fama da rikice-rikice da ke haddasa asarar ɗimbin rayuka.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1490 days 8 hours 4 minutes 47 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1472 days 9 hours 46 minutes 12 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com