KAROTA ta kama direban motar da ya taka fulawar da ake kawata titunan birnin Kano

Hukumar kula da zirga-zirga ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta kama direban wata motar gida saboda zarginsa da karya dokar tuki.

Hukumar ta KAROTA ta kama direban ne akan titin Murtala Muhammad dake birnin Kano bayan ya tsallaka titin ta wajen da bai dace ba, tare da taka fulawar titi da gwamnatin Kano ta kawata titin da su.

A wata ganawarsa da manema labarai mai magana da yawun hukumar ta KAROTA Malam Abubakar Ibrahim Sharada yace direban ya karya dokar hanya kuma za’a gabatar dashi a gaban kotu domin zama izinina ga masu kokarin karya dokar tuƙi a jihar.

Daga bisani Yaja kunne direbobi da su guji karya dokar hanya, yana mai cewa hukumar ta KAROTA ba zata zura idanu ba.

An zargin Direban da yiwa Jami’an hukumar gadara.

Tunda farko mai baiwa gwamnan Kano shawara kan harkokin yada Labarai Hon Ibrahim Adam shine ya wallafa yadda diraban ya karya dokar tukin, kuma hakan yaja hankalin hukumomin da abin ya shafa aka kamo diraban.

Ko dai a watan da ya gabata sai da gwamnatin Kano ta gurfanar da wasu masu awakai a gaban kotu saboda lalata cikawar da suka yi.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1491 days 9 hours 3 minutes 0 second,

Baptist School Students, Kaduna
1473 days 10 hours 44 minutes 25 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com