Sanatocin PDP 4 sun sauya sheƙa zuwa APC a Najeriya

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio yau ya sanar da cewar ƴan majalisu guda hudu ne daga jam’iyyar PDP suka sauya sheka zuwa APC mai mulki.

Akpabio wanda ya karanta wasikar da kowanne ɗaya daga cikin su ya rubuta wa majalisar, ya ce matsayin na su ya biyo bayan rashin fahimtar juna daga jam’iyyar ta su, wadda ke fama da rikicin cikin gida.

Ƴan majalisun sun hada da Anieken Bassey daga mazaɓar Akwa Ibom ta Arewa maso gabas da Samson Ekong daga mazabar Akwa Ibom ta kudu da Francis Fadahunsi daga osun ta gabas da kuma Oluwole Olubiyi daga Osun ta tsakiya.

Sakamakon wannan sauyin, adadin Sanatocin APC ya kai 70 a zauren Majalisar Dattawa, yayin da PDP ke da kujeru 28, sai kuma Labour mai 5, SDP guda 2, sannan kuma NNPP da APGA na da guda guda.

Tuni masu sanya ido a siyasar Najeriya suka fara bayyana fargaba a kan makomar siyasar ƙasar musamman ganin yadda ta kama hanyar komawa kasa mai jam’iyya guda tare da rushewar adawa.

Wannan ya biyo bayan gazawar shugabannin jam’iyyar PDP wadda ta kwashe shekaru 16 tana jagorancin ƙasar, kafin rasa kujerar shugaban ƙasa a shekarar 2015 na haɗa kan ƴƴanta domin tafiya tare.

Yanzu haka wasu jiga jigan ta da dama sun koma APC inda ake damawa da su, cikin su harda shugaban majalisar dattawan Akpabio da ya yi gwamnan shekaru 8 a ƙarƙashin tikitin PDP.

A baya bayan nan wasu gwamnoni da ƴan majalisu a matakai daban daban da suka samu kujerun PDP a zaɓen da ya gabata, duk sun yi watsi da jam’iyyar domin komawa APC mai mulki.

Shi babban madugun tafiyar PDPn kuma tsohon matamakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da ya yi mata takarar zaben shekarar 2023 ya sanar da ficewar sa a makon jiya, abinda wasu ke kallo a matsayin matakin ƙarshe na rugujewar PDP.

Sai dai wasu na bayyana fatar ganin sabuwar ƙawancen  yan adawar a jam’iyyar ADC watakila ka iya taka rawa wajen tikarar APC idan jiga jigan ta suka haɗiye maitar su ta neman shugabanci domin fafatawa da APC a zabe mai zuwa.

Yanzu haka rahotanni na dada nuna cewar APC na zawarcin daya ɗaga cikin fitattun yan siyasar ƙasar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, domin ƙara karfi kafin zabe mai zuwa.

Ko a ranar litinin da ta gabata, sanda aka yi wata ganawar sirri tsakanin shugaban ƙasa Bola Tinubu da Kwankwason a fadarsa, amma kuma babu wani cikakken bayani a kan abinda suka tattauna ko matsayar da suka cimma.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1498 days 7 hours 37 minutes 27 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1480 days 9 hours 18 minutes 52 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com