Bincike: Shin da Gaskiya ne Gadar Sama da aka gidana kan Naira Biliyan 10 a Lafia, dake jihar Nasarawa ta Rushe Bayan Mako Uku da Kaddamar da Ita?

Bincike: Shin da Gaskiya ne Gadar Sama da aka gidana kan Naira Biliyan 10 a Lafia, dake jihar Nasarawa ta Rushe Bayan Mako Uku da Kaddamar da Ita?

Ikirari: Wani hoto da ke yawo a shafukan sada zumunta kamar X (wanda aka fi sani da Twitter), Facebook da Instagram ya nuna cewa sabuwar gadar sama da aka kammala gina wa a Lafia, dake jihar Nasarawa, wadda aka kasha zunzurutun kudi har Naira biliyan 10 a kanta, ta rushe mako uku bayan kaddamar da ita.

Saƙon da ke tare da hoton yana cewa: “DA ƊUMI-ƊUMI: Gadar sama ta rushe bayan mako uku da kaddamar da ita a Lafia, Jihar Nasarawa. An kashe biliyan 10 a aikin. Nijeriya Kenan.”

Wannan ikirari ya jawo cece-kuce gami da nuna damuwa daga ‘yan Najeriya a shafukan sada zumunta, inda da dama ke kallon hakan a matsayin alamar cin hanci da rashin ingancin ayyukan gine-gine a ƙasar.

Lokacin da hoton ya bayyana da kuma tsananin mahawara da ake yi kan ingancin ayyuka a Nasarawa ya sa jama’a suka yi tunanin cewa gadar Lafia da aka kaddamar a watan Mayu 2025 da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya halarta, ta rushe.

Tabbatar da sahihancin Ikirari: Tawagar bincike ta PRNigeria ta gudanar da bincike mai zurfi don tabbatar da sahihancin ikirarin, inda ta gano cewa ikirarin ya fara yaduwa a ranar 23 ga Yuli, 2025.

Binciken ya gano cewa wannan ikirari ya fito ne bayan wani tabbataccen al’amari na rushewar wani sashi na gadar sama a Keffi, jihar Nasarawa. A ranar 18 ga Yuli, 2025, inda wata motar daukar kaya ta gugi  wani bangare na  turakun gadar, wanda hakan ya haifar da rushewar wani sashi na gadar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum biyu da jikkatar wasu. A dalilin haka ne Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin gyaran gaggawa na kwanaki 30 a wurin.

Wannan aikin da aka ce ya ci Naira biliyan 10 a zahiri ya ci Naira biliyan 16, kuma an kaddamar da shi ne a watan Mayu 2025, bisa halartar shugaba Tinubu da Gwamnan jihar Abdullahi Sule. Wadda ita ce gadar farko da aka gina a matsayin gada ta sama a birnin Lafia, kuma an kirkiro ta ne domin rage cunkoso da inganta zirga-zirgar ababen hawa a birnin.

Haka kuma, sakamakon bincike ta hanyar duba hoton da ake yadawa ya nuna cewa an taba amfani da shi a wasu lokuta daban-daban da ba su da alaka da Najeriya, ciki har da matsayin hoto na bogi da ke nuna wani bala’in gadar da aka ce ya faru a Bihar, India. Ko da yake an samu wani rushewar gada na gaske a Indiya a cikin wannan watan, amma ba shi ne hoton ba.

Nazarin hoto da kayan aikin tantance hotunan AI ya bayyana alamun karya kamar: karkacewar tsari, yanayin inuwa, da rashin cikar sifar mutanen dake hoton wadanda duk alamomi ne na hoton da aka kirkira da manhajar fasahar AI.

Kari a kan haka, babu wani rahoto daga kafafen yada labarai masu zaman kansu ko gwamnatin Nijeriya da ya tabbatar da wannan hoto ko faruwar lamarin.

Kammalawa: Binciken PRNigeria ya tabbatar da cewa babu wata hujja da ke nuna cewa gadar sama ta Lafia ta rushe. Hoton da ke yawo hoton kirkira ne da aka samar ta hanyar AI, kuma an taba amfani da shi a labaran ƙarya a wasu ƙasashe. Duk da cewa an samu wani rushewar gada na gaske a Keffi, babu abu da ya shafi gadar Lafia.

Hukunci: Labarin da ake yadawa KARYA NE

Hoton da ke yawo da ikirarin rushewar gadar sama a Lafia, jihar Nasarawa, karya ne kuma yana da niyyar yaudarar jama’a. Hoton na bogi ne da aka kirkira da fasahar AI.

Daga PRNigeria

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1499 days 17 hours 37 minutes 55 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1481 days 19 hours 19 minutes 20 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com