Yadda Hukumar KAROTA ta karbi koken direbobin mota a jihar Kano

Wasu daga cikin Direbobin Bus a Jihar Kano sun koka bisa yadda Jami’an Hukumar Karota ke matsa mutsu Jahar.

Wannan na cikin wata sanarwa da Mai Magana da yawun hukumar ta KAROTA Abubakar Ibrahim Sharada ya fitar ya kuma aikewa manema labarai a jihar Kano.

Direbobin sun kai Koken ne a shalkwatar Hukumar ta lura da zirga-zirgar ababawan ta jihar Kano da nufin a duba domin magance masu matsalar.

Jagoran ayarin Kungiyar Matasan Direbobi ta Garin Kunya dake yankin Karamar Hukumar Minjibir, Mumfadalu Bukar Sakatare Ya koka bisa yadda jami’an Hukumar Karota Ke yawan kama Motocin Bus a duk lokacin da suka fito don gudanar da sana’ar su.

“Duk da cewar yanzu Direbobin a Daidaita Sahu sun Kwace mana akasarin Fasinjojin da mu direbobin Bus muke dauka hakan bata sanya Jami’an Karota sun saurara mana ba wajen kame Motocin mu”, inji Mumfadalu Sakatare.

“Tun da gwamatin Jahar Kano mai ci yanzu ta dagawa Direbobin A Daidaita Sahu kafa, to muma Direbobin Bus mun cancanci wani karamci na Gwamnati wajen karbar Kudaden shiga.” a cewar Jagoran Direbobin na Matasan Kunya.

Yana magane kan Kudaden Sticker wanda ya ce akan haka Jami’an Hukumar KAROTA Ke yawan kame motocin su.

A jawabin sa, Shugaban Hukumar KAROTA, Hon Faisal Mahmud Kabir ya yabawa Kungiyar Matasan Direbobi ta Garin Kunya bisa Kawo wannan koke da suka yi, a madadin sauran Direbobin Bus.

Manajan Daraktan wanda Daraktan kula da harkokin Kudaden shiga na Hukumar KAROTA, Alh Nura Ahmad Diso Ya wakilta yace abinda direbobin suka kawo koke akan sa hurumi ne na Gwamnatin Tarayya, don haka ya shawar ce su dasu miƙa Koken zuwa Hukumar tattara Kudaden Haraji ta Jahar Kano don magan ce al’amarin.

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1499 days 11 hours 53 minutes 29 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1481 days 13 hours 34 minutes 54 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com