Wasu rahotannin na bayyana cewa Ƴanbindiga sun kashe wasu mutum 38 ta hanyar yi musu yankan rago, daga cikin mutum 56 da suka yi garkuwa da su sakamakon gaza biyan kuɗin fansa da ƴanbindigar suke nema.
Mutanen da aka kashe ɗin sun kasance ƴan ƙauyen Banga da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar ƙauran Namoda da ke jihar Zamfara.
kafara BBC ta rawaito yadda Shugaban ƙaramar hukumar, Manniru Haidara Ƙaura wanda ya shaida mata yadda al’amarin ya faru, ya ce yawancin waɗanda aka yi wa yankan ragon matasa ne.
“Bayanin da muka samu shi ne sun yi musu yankan rago ne. Abin da ya faru shi ne ƴanbindigar sun nemi kuɗin fansa kuma aka harhaɗa aka ba su kamar yadda suka nema, inda kuma suka saki mutum 18 da suka haɗa da mata 17 da ƙaramin yaro guda ɗaya, a ranar Asabar,”in ji Haidara.
Kimanin watanni huɗu ne dai ƴan fashin daji suka far wa ƙauyan na Banga da ke ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda a jihar ta Zamfara inda suka yi garkuwa da mutum 56.
Read Also:
“Bayanan da suka zo mana shi ne ƴanbindigar sun nemi kuɗin fansa na naira miliyan 50 kuma an ba su amma duk da haka suka zaɓi su kashe mutum 38. Su suka san dalilin kashe su. Mutane ne da ba su da tunani da ba su da hankali. Sun manta ƴanuwansu ne suke kashewa kuma za mu haɗu a gaban Allah.”
Shugaban ƙaramar hukumar ya kuma ƙara da cewa kawo yanzu mutum 16 da suka dawo da su ranar Asabar na asibiti inda ake kula da lafiyarsu, inda gawar su kuma mutum 38 da aka kashe na wurin ƴanbindigar “kamar yadda suka saba ai ba sa bayar da ita.”
Dangane kuma da abin da ya shafi jami’an tsaro a yankin, Manniru Haidara Ƙaura ya ce duk da a wasu wuraren yana jin labarin irin ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi amma a yankinsa labarin ya sha banban.
“Alal haƙiƙanin gaskiya jami’an tsaro ba sa ba mu irin tallafin da ya kamata mu samu daga ɓagarensu ba ma samu….illa dai askarawa na jihar Zamfara su ne kawai suke taimakon mu.”
Jami’an tsaron Najeriya dai musamman sojoji sun sha musanta zarge-zargen da ake yi musu na rashin ka ɗauki a wuraren hare-hare, inda suke cewa jama’a ne ba sa sanar da su da wuri sannan a mafi yawancin lokuta mutane ba su san irin koƙarin da suke yi ba.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1502 days 5 hours 49 minutes 53 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1484 days 7 hours 31 minutes 18 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com