Gwamnan Zamfara ya Amince da Nadin Sabon Sarki Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da nadin Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin Sarki na 16 na Masarautar Gusau, wanda ya gaji mahaifinsa, Marigayi Dr. Ibrahim Bello, da ya rasu a ranar 25 ga Yuli bayan shekaru goma yana sarauta.

Nadin ya biyo bayan shawarwarin masu zaben sarki na masarautar Gusau, tare da bin al’adun gargajiya da dokoki na kasa.

Alhaji Abdulkadir, wanda shi ne babban ɗan marigayi sarki, yana rike da sarautar Bunun Gusau kafin wannan nadin. Shi ɗan asalin Malam Sambo Dan Ashafa ne.

Gwamna Dauda Lawal ya taya sabon sarki murna tare da kira gare shi da ya ci gaba da gadon kyakkyawar rayuwa da dabi’un sarakunan da suka gabata, wanda zai zama jigo wajen ɗorewar zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba a masarautar Gusau da ma kewaye

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com