Gwamnan Kano ya aikewa Majalisar dokoki sunan wanda zai shugabanci hukumar yaki da cin hanci da rashawa

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya turawa Majalisar dokokin jihar Kano sunan Sa’idu Yahya domin tantance shi don nada shi a matsayin shugaban hukumar Karbar korafe-korafe da Hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban daraktan yada labaran gwamnan kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fita ya kuma aikewa PRNigeria.

Idan za’a iya tunawa a makon nan ne wa’adin aikin tsohon Shugaba hukumar Muhuyi Magaji Rimin Gado ya Cika, inda bayan ya sauka aka nada Zaharadden Hamisu Kofar mata a matsayin shugaban hukumar na rikon kwarya.

Ya ce Sa’idu Yahya Ƙwararre ne kuma masani a Kan harkar yaki da cin hanci da rashawa, inda yayin aiki a hukumar dake yaki da rashawa ta ICPC.

Ya ce ya rike mukamai da dama kuma ya na da Kwarewa Sosai ta yadda zai yaki cin hanci da rashawa.

Sanarwar ta ce Wanda aka baiwa mukamin Rikon kwaryar Wato Zaharadden Hamisu Kofar Mata an mayar da shi ma’aikatar Harkokin shari’a ta jihar Kano.

Gwamnan ya yabawa Muhuyi bisa yadda ya Jagoranci hukumar da kuma gudunmawar da ya bayar wajen yaki da cin hanci da rashawa a jihar Kano.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com