Home Labarai Tinubu ya yi karin wa’adin Aiki ga shugaban Custom na Nijeriya

Tinubu ya yi karin wa’adin Aiki ga shugaban Custom na Nijeriya

Shugabn Nijeriya Bola Tinubu ya karawa shugaban hukumar hana fasa kwauri ta kasa (Custom) Bashir Adewale Adeniyi wa’adin aiki na shekara guda.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da wa’adin aikin nasa zai kare karshen wata mai kamawa wato 31 ga watan Agustan 2025.

Ta cikin wata sanarwa daga Fadar Shugaban Ƙasa da Bayo Onanuga, Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan Harkokin Bayani da Tsare-tsare, ya sanya wa hannu, wadda ta ce ƙarin wa’adin na da nufin bai wa Adeniyi damar kammala sauye-sauyen da ake aiwatarwa tare da cika manyan manufofin gwamnatin Bola Tinubu.

Ayyukan  da ake son kammalawa sun haɗa da sabunta tsarin aikin Hukumar Kwastam, aiwatar da tsarin National Single Window Project, da kuma cika alƙawarin da Najeriya ta ɗauka a ƙarƙashin yarjejeniyar ciniki ta nahiyar Afirka (AfCFTA).

Shugaba Tinubu ya yabawa Adeniyi bisa “ƙwazo da ya nuna wajen jagoranci da da kuma hidimatawa,” yana mai bayyana tabbacin cewa ƙarin wa’adin zai ƙarfafa rawar da Hukumar Kwastam ke takawa a fannin sauƙaƙe cinikayya, haɓaka kuɗaɗen shiga, da kuma tsaro a kan iyakoki Nijeriya.

PRNigeria

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp