Ambaliyar ruwa ta yiwa wasu jihohin Arewa barna

Ambaliya ta cinye gonaki da gidaje da makarantu da wuraren ibada a jihohin Bauchi da Filato da kuma jihar Neja, lamarin da ya tilasta wa ɗaruruwan mutane barin gidajensu.

Mazauna yankunan da lamarin ya faru sun ce ruwan saman da aka samu kamar da bakin ƙwarya haɗe da iska a wayewar garin ranar Lahadi, ya kayar da bishiyoyi tare da tsige turakun lantarki da ɗaye kwanukan rufi lamarin da ya sa gine-gine da dama suka faɗi.

akalla gine-gine 50 ne suka rushe sakamakon ambaliyar a garin Menkaat na ƙaramar hukumar Shendam a jihar filato.

Can a ƙaramar hukumar Dass ta jihar Bauchi fiye da magidanta 40 suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar da ta lalata gonaki masu yawa a cewar Jaridar.

Haka a jihar Neja kusan garuruwa 18 ne suka fuskanci ambaliyar a ƙaramar hukumar Lapai ta jihar Neja, inda ruwa ya cinye gonaki masu yawa.

Lamarin na zuwa ne dai a daidai lokacin da hukumar hasashen yanayi ta ƙasar, (Nimet) ke gargaɗin samun ruwan sama haɗe da tsawa da yiwuwar samun ambaliya a wasu jihohin ƙasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com