Za mu gurfanar da masu karya dokokin hanya a jihar Kano – KAROTA

Hukumar dake lura da zirga-zirgar ababan hawa a jihar Kano (KAROTA) tayi barazanar gurfanar da dukkan direba ko matukin adaidaita sahu da ya karyar dokokin tuki a kan hanyoyin jihar a gaban kotu domin yi masa hukuncin.

Wannan dai na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Jami’in yada labaran hukumar Abubakar Ibrahim Sharada ya aikewa PRNigeria, wadda ta ambaci shugaban hukumar Hon. Engr. Faisal Mahmud Kabir na yin gargadin musamman masu ta’adar saba dokokin fitilar mahadar tititunan jihar (Traffic Light) idan an tsayar da su.

wannan na gargadi dai na zuwa ne kwana guda bayan Umarni na Musamman da mai girma gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bai wa KAROTA, dangane da tabbatar da bin dokokin Fitilun ba da hannu akan hanyoyi da aka sanya a manyan titunan cikin birnin Kano.

Hon. Faisal ya tabbatar da cewa hukumar za ta aiwatar da umarnin Gwamna dari bisa dari, la’akari da cewa gwamnatin Kano na kashe kuɗi masu yawa wajen saka Fitilun ba da hannun da ke amfani da hasken rana domin inganta zirga-zirga a cikin birni.

“Ina so in yaba wa mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa kulawarsa ga jin daɗin al’ummar Kano, ta hanyar girka waɗannan fitilun Bada hannu akan hanyoyi Masu amfani fa hasken rana da za su rika aiki sa’o’i ashirin da huɗu a kowace rana a kan titunanmu,” inji shi.

Saboda haka, Shugaban ya buƙaci al’ummar jihar, musamman direbobi, da su ba da haɗin kai ga jami’an KAROTA yayin da suke amfani da tituna, domin samun kyakkyawar alaƙa da jama’a.

Ya bayyana cewa, shawarar mai girma Gwamna na dawo da fitilun ba da hannu a manyan tituna da cikin gari na nufin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, don haka ya dace kowa ya mutunta wannan tsari ta hanyar bin umarnin ba da hannu da wadan nan Fitulun ke yi akan hanyoyin mu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com