Kwamishinan sufurin jihar Kano da ke arewa maso gabashin Najeriya ya ajiye muƙaminsa kan zargin alaƙarsa da mutumin da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a jihar.
Gwamnatin jihar Kano ce ta sanar da murabus ɗinsa a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Laraba.
Ibrahim Ali Namadi ya ajiye muƙaminsa na kwamishina ne bayan gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin binciken zarginsa da hannu a belin Sulaiman Aminu Danwawu, wanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a jihar.
Batun belin Danwawu da ake zargin da hannun kwamishinan, ya ja hankalin jama’ar Kano da ma Najeriya.
“Kwamishinan ya ce ya yanke shawarar yin murabus ne saboda buƙatar al’umma da kuma tasirin al’amarin.”
Sai dai a sanarwar, Kwamishinan ya ci gaba da kare kansa a matsayin marar laifi tare da nisanta kan shi da zargin da ake masa.
“Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus ɗin kwamishinan, tare da yi masa fatan alheri,” kamar yadda Sunusi Bature Dawakin Tofa ya tabbatar