Gwamnatin Najeriya ta yi hasashen za a shafe kwana biyar ana ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ka iya janyo afkuwar ambaliyar ruwa a sassan jihohi 19 da kuma wasu wurare 76 a ƙasar.
Gargaɗin da aka fitar daga ma’aikatar muhalli ta ƙasar, ya buƙaci masu ruwa da tsaki da kuma mazauna yankunan da lamarin ka iya shafa da su ɗauki matakan kariya.
Hakan na zuwa ne yayin da mummunar ambaliya ta afku a jihohin Ogun da Gombe yayin da wasu jihohin da suka haɗa da Legas da Filato da Anambra da Delta suma matsalar ta shafe su.
A cewar sanarwar, ana hasashen yankunan za su samu mamakon ruwan sama a yankunan da zai iya haifar da ambaliya daga 5 zuwa 9 ga watan nan na Agusta.
Jihohin da hasashen ya shafa sun haɗa da Akwa Ibom da Bauchi da Ebonyi da Cross River da Nasarawa da Benue da Kaduna da Katsina.
Sauran jihohin sun haɗa da Kebbi da Kano da Neja da Filato da Taraba da Jigawa da Yobe da Zamfara da Sokoto da Borno da Gombe.
Matsalar ambaliya a Najeriya ta zama ruwan dare kowace shekara wadda ke janyo asarar rayuka da salwantar dukiya mai yawa.
A bara, jihohi 31 rahotanni suka bayyana sun yi fama da bala’in ambaliya da ta shafi mutum miliyan 1.2.