Fadar Shugaban ƙasa ta musanta raɗe-raɗin rashin lafiyar Tinubu

Hoton Tinubu

Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta musanta rahotannin da ke nuna cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ba shi da lafiya kuma ana shirin fitar da shi zuwa asibiti a ƙasar waje.

A makon da ya gabata ne dai cibiyar aikin jarida mai binciken ƙwaƙwaf ta Najeriya, ICIR ta rawaito cewa wasu majiyoyinta sun tabbatar mata da cewa tawagar likitocin shugaban ƙasa na ta shirye-shiryen fitar da shugaba Tinubu zuwa ƙasar wajen domin neman magani.

Cibiyar kamar dai yadda ta wallafa a shafinta na intanet ta ce “rahotanni na nuna cewa shugaba (Tinubu) na kwance a gado ba ya iya zuwa ko’ina abin da ya janyo rashin gudanar da al’amuran shugabanci. Mataimakinsa, Kashim Shettima ya wakilci shugaban a wasu ayyukan gwamnati.”

ICIR ta kuma rawaito wani jami’i a fadar shugaban ƙasar da ke cewa an soke aikace-aikace da dama da ya kamata shugaban ya gudanar a farkon makon da ya gabata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com