Ƙananan dillalan mai sun zargi shugabanninsu da yiwa Matatar Dangote zagon ƙasa

Ƙananan dillalan man fetur a Najeriya sun zargi shugabannin su da neman yiwa Matatar Dangote zagon ƙasa a yunƙurin ta na jigila da kuma rarraba tataccen mai zuwa sassan ƙasar.

Daya daga cikin ƙananan dillalan Alhaji Ladan Abdullahi Garkuwa ya ce matakin na Dangote zai bai wa masu ƙaramin ƙarfi irin su damar dawo da karsashin su na dillancin man, la’akari da cewar tsadar man ya sa basa iya sayensa kamar yadda suke yi a baya.

Garkuwa ya ce da yana da gidajen mai guda biyar yanzu haka, amma tsadarsa ya sa ba ya iya sayen mota guda da zai sayar.

Dillalin ya ce yanzu da wannan sabon tsari na Dangote wanda zai dinga kai musu man kai tsaye zuwa gidajen man su, inda har sai sun sayar su biya shi, matakin zai ba shi damar karbar man a gidajen man sa guda biyar domin ci gaba da kasuwancinsa.

Dan kasuwan ya ce wannan mataki zai ba shi damar ɗaukar ƙarin ma’aikata waɗanda su ma za su amfana da tsarin, wadda za ta taimaka wajen sauƙaƙa wahalar man.garkuwa ya ce abin takaici ne yadda manyan dilallan man ke adawa da shirin Dangoten, wanda suke kallonsa a matsayin babbar barazana ga harkokin su, musamman  ganin yadda suka mamaye harkar man suke kuma cin karen su babu babbaka.

Tuni matatar Dangote ta karɓi wasu daga cikin motocin da ta sayo daga ƙasar China da za su yi aikin jigilar man zuwa sassan Najeriya, a yunƙurin sauƙaƙawa jama’ar ƙasar samun tacaccen man da suke sarrafawa.

A baya, manyan dillalan man a Najeriya, sun gabatar da ƙorafin adawa da shirin Dangote na sayo motocin da za su dinga safarar man, inda suka zarge shi da yunƙurin mamaye kasuwar.

Wanan bai sanya Dangoten ƙasa a gwuiwa ba, wajen ci gaba da sayo motocin waɗanda tuni suka isa Najeriya domin fara aiki.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com