EFCC ta ba da belin tsohon gwamnan Sokoto Tambuwal da ta tsare

Hukumar da ke yaki da yi wa masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa a Najeriya EFCC ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, bayan ta yi masa tambayoyi kan wawushe dukiyar ƙasa da ya kai sama da Naira biliyan 189.

An gayyaci Tambuwal wanda ya mulki jihar Sokoto daga shekarar 2015 zuwa 2023, zuwa hedikwatar EFCC da ke Abuja ranar Litinin, inda ya isa da misalin karfe 11:30 na safe.

Masu bincike sun yi masa tambayoyi kuma daga baya aka tsare shi a shelkwatar hukumar.

Majajiyoyi sun ce, a ranar Talata, aka saki tsohon gwamnan bayan cika sharuddan belinsa, waɗanda aka bayyana a matsayin mara tsauri.

Ƴan adawa sun bayyana tsare tsohon gwamnan da EFCC ta yi, a matsayin wani yunƙuri na karya lagon ƴan adawa da gwamnati maici a ƙasar ke yi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com