Hukumar KAROTA ta kaddamar da kotun tafi da gidanka a jihar Kano

Hukumar dake lura da zirga-zirgar ababan hawa ta jihar Kano KAROTA ta kaddamar da kotunan tafi da gidanka a jihar.

Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Abubakar Ibrahim Sharada Anipr ya aikewa PRNigeria, in da sanarwar ta ce hukumar ta dauki matakin ne don yankewa direbobi da ke karya dokar fitilun bada hannu a manyan titunan birni kano.

Da yake kaddamar da kotunan, Manajan Darakta na KAROTA, Hon. Faisal Mahmud Kabir, ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan umarnin da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bai wa hukumar domin tabbatar da bin dokokin zirga-zirga daga direbobi da masu tukin adaidaita sahu a jihar.

Manajan Daraktan ya jaddada cewa ganin yadda gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta zuba makudan kudade wajen girka sabbin fitilun hasken wuta masu amfani da rana (solar), dole ne masu ababen hawa su nuna godiya ta hanyar bin doka da odar.

ya kuma Ya ja kunnen duk direban da aka kama yana karya dokar cewar jami’an KAROTA tare da hadin gwiwar jami’an tsaro za su cafke shi domin a gudanar da shari’a nan take a gaban kotun tafi-da-gidanka.

PRNigeria

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com