Shalkwatar tsaron Nijeriya ta yi karin bayani kan batun kare kai

Shalkwatar tsaron Najeriya ta yi ƙarin haske kan kalaman da babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya yi kan batun kare kai daga hare-haren ƴan fashin daji.

Cikin wata sanarwa da shalkwatar tsaron ta fitar ta ce kalaman Janar Musa ba suna ƙarfafa wa mutane mallakar makami ba ne, kamar yadda wasu kafofin labarai a ƙasar ke yaɗawa.

”Abin da yake nufi shi ne ƴan ƙasa su koyi dabarun kare kai da duniya ta amince da su kamar ƙwarewar tuƙi, da judo da ninƙaya da dambe ko kokawa da sauransu”, in ji sanarwar.

‘Kalamansa ba sa nufin mallakar makami ta haramtacciyar hanya, saboda yana sane da dokokin Najeriya da suka haramta mallakar makami”.

A ranar Alhamis ne cikin wata hira da gidan Talbijin an Channels, Janar Musa ya ce ya kamata kowane ɗan Najeriya ya koyi dabarun kare kai domin kauce wa hare-haren ƴanbindiga.

Kalaman babban hafsan dai sun janyo ce-ce-ku-ce tsakanin ƴan ƙasar inda wasu ke ganin hakan na nuna gazawa a ɓangaren gwamnati na magance matsalar rashin tsaron da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com