Gwamnatin Chaina ta bayar da tallafin dala miliya 1 domin tallafawa wadanda matsalar ambaliyar ruwa ta shafa a yakin arewacin Nijeriya.
Ministan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki na kasar Abubakar Atiku bagudu ne ya bayyana hakan yayin da suke musayar sanya hannu da Ambasan kasar China Yu Dunhai a birnin tarayya Abuja.
Read Also:
Sanata Atiku Bagudu ya bayyana cewa tallafin na kasar Chaina ya zo a lokacin da ake bukatarsa, yana mai jaddada cewa hakan zai taimaka wajen karfafa kokarin gwamantin tarayya na isar da kayan agaji da farfado da rayuwar al’ummar da ambaliyar ta fi shafa.
“Muna da yakinin cewa bikin sanya hannu da muka yi a yau zai bude sabbin hanyoyin hadin gwiwa, da karfafa zumuncinmu domin amfanin dukkan jama’ar kasashenmu,” in ji Bagudu.