Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya karyata jita-jitar cewa yana shirin komawa APC ko shiga sabuwar kawance a jam’iyyar ADC.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar na kasa yau, inda ya ce zai ci gaba da kasancewa a cikin NNPP.
Read Also:
Jam’iyyar ta shiga rikicin shugabanci tun bayan babban taron da wani bangare ya gudanar a Fabrairu, wanda ya janyo rabuwar kawuna tsakanin magoya bayan Kwankwaso da kuma wasu daga cikin mambobin da suke ikirarin kafa jam’iyyar.
A kwanakin baya, bangaren Agbo Major ya bukaci INEC ta dage zabuka kan rikicin tambarin jam’iyyar.
Kwankwaso ya ce jam’iyyar za ta sanar da matakinta a lokacin da ya dace.