Sojojin Najeriya tare da jami’an tsaron farin kaya (DSS) sun kashe aƙalla ƴan bindiga 50 sannan kuma suka kuɓutar da wasu daga cikin mutanen ake garkuwa da su a ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja.
Jami’an tsaron sun ce sun yi arangama da kusan ƴan bindiga 300 ɗauke makamai a ranar 26 ga Agusta, bayan sun yi ƙoƙarin kai hari a ƙauyen da kuma kai farmaki a sansanin DSS.
“Gaskiya ne, shekaran jiya ne muka samu rahoton fitowar ‘yan bindiga daga jihar Zamfara suna tunkarar yankunanmu daga Katonkoro zuwa Kumbashi har zuwa Gulbin Boka.”
“Amma kafin su isa, mun sanar da jami’an tsaro da muke da su, ciki har da sojoji da ‘yansanda, da DSS, waɗanda suka yi iyakar ƙoƙarinsu wajen tare su domin hana su kai farmaki wuraren da suka saba.”
Amma kuma ya ce ƴan bindigan sun samu hanyar shiga Gulbin Boka inda suka yi garkuwa da mutane da dama.
“Amma a hanyarsu ta komawa Zamfara, mun haɗa hannu da jami’an DSS a Kumbashi, inda muka fatattake su kuma muka kuɓutar da mutanen da aka sace, tare da ƙwato wasu dukiyoyin da suka sace”
Abbas ya tabbatar da cewa ba a samu asarar rai daga ɓangaren mutanen gari ba, amma jami’ai sun hallaka kusan ‘yan bindiga 50 tare da ƙona dukkan baburansu.
“Sai dai kuma an samu hasarar rayuka a cikin jami’anmu.” in ji shi.
Wannan lamari ya biyo bayan kama Abubakar Abba, shugaban kungiyar dabar Mahmuda a yankin Wawa na jihar, wanda DSS ta yi a kwanan nan.